Hausa translation of the meaning Page No 407

Quran in Hausa Language - Page no 407 407

Suratul Al-Rum from 25 to 32


25. Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita.
26. Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a gare Shi.
27. Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
28. Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki- daki, ga mutãne mãsu hankaltawa.
29. Ã'aha! waɗanda suka yi zã1unci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba. To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?
30. Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, ( 1 ) kanã mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah, wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
31. Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai. ( 2 )
32. Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya- ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.
( 1 ) Yin addini ɗabĩ'a ce wadda Allah Ya halitta mutum akanta. Idan mutum ya bi abin da Allah Ya umurce shi dayikõ bari, to, yã yi addinin gaskiya, idan kuwa bai yi haka ba, ya zama mushiriki game da wanda yake karɓar umurni daga gare shi.
( 2 ) Ya fassara mushirikai da ãyã ta 32. Wannan ya nũna ta yi nũni ga hana dukkan ɗarĩƙun sũfãye dõmin sunã rarraba mutãne ƙungiya- ƙungiya, kuma kõwa nã ganin abin da yake yi ko kuma wanda yake bi yã fi na wani. Kumawanda ke cikin wata ƙungiya bã zai iya haɗuwa da wata ba a lõkacin wurudinsu, a bãyan abũbuwan da suke ƙunsãwa a cikin ayyukansu na bidi'õ'i da aƙĩdõdi da suka sãɓa wa Musulunci.