Hausa translation of the meaning Page No 409

Quran in Hausa Language - Page no 409 409

Suratul Al-Rum from 42 to 50


42. Ka ce: « Ku tafi a cikin ƙasã sa'an nan ku dũbi yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance mãsu yin shirki. »
43. Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa ( su rabu biyu ) .
44. Wanda ya kãfirta,to,kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa.
45. Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai.
46. Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, fãtanku zã ku gode.
47. Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi, kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu.
48. Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi.
49. Kuma kõ da sun kasance a gabãnin a saukar da shi a kansu, kusa- kusa, sunã baƙin ciki hai bã su iya magana.
50. Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle wannan ( Mai wannan aiki ) , tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kõme.