Hausa translation of the meaning Page No 408

Quran in Hausa Language - Page no 408 408

Suratul Al-Rum from 33 to 41


33. Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu.
34. Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku, sani.
35. Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka kasance sunã shirkin da shi?
36. Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã yanke ƙauna,
37. Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni.
38. Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
39. Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar Allah to ( mãsu yin haka ) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa ( ga dũkiyarsu ) .
40. Allah ne Wanda Ya halitta ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki.
41. Ɓarnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su kõmo.