Hausa translation of the meaning Page No 410

Quran in Hausa Language - Page no 410 410

Suratul Al-Rum from 51 to 60


51. Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle zã su yini a bãyansa sunã kãfirta.
52. Sabõda haka, kai, bã ka jiyar da matattu kira, kuma bã ka jiyar da kurãme kira idan sun jũya bãya sunã gudu.
53. Kuma ba ka zamo mai shiryar da makãfi ba daga ɓatarsu, bã ka jiyarwa fãce wanda ke yin ĩmãni da ãyõyinMu, watau sũ ne mãsu mĩƙa wuya, su sallama.
54. Allah ne Ya halitta ku daga rauni, ( 1 ) sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi,
55. Kuma a rãnar da Sa'a ( 2 ) ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su.
56. Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: « Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar, kuma amma kũ, kun kasance ( 3 ) ba ku sani ba. »
57. To, a rãnar da uzurin waɗanda suka yi zãlunci bã ya amfaninsu, kuma bã a neman yardarsu.
58. Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta zã su ce « Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua. »
59. Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba.
60. Sabõda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda bã su da yaƙĩni su sassabce maka hankali.
( 1 ) Raunin farko, shĩ ne maniyyi, na biyu jãruntaka da ƙarfin ƙurũciya, rauni na uku, shi ne tsũfa bãyan ƙarfin hankalin kamãla ta dattãko.
( 2 ) Sa'a ta farko Rãnar Ƙiyãma,ta biyu ɗan lõkaci, watau ɗan lõkacin da suka sãmi hutun azãbar kabari a tsakãnin bũsar farko da ta biyu. Akwai munãsabar ƙaryarsu ta dũniya da ta Lãhira. Akwai munasabar dangantakar lafazin kalmomi.
( 3 ) Rashin aiki da littãfin Allah a dũniya yakan sanya ɗĩmuwa a rãnar Lãhira.