Hausa translation of the meaning Page No 419

Quran in Hausa Language - Page no 419 419

Suratul Al-Ahzab from 7 to 15


7. Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama,kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su.
8. Dõmin Ya tambayi mãsu gaskiya a kan gaskiyarsu, kuma Yã yi tattalin wata azãba mai raɗaɗi ga kãfirai.
9. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da waɗansu rundunõni suka zo muku, sai Muka aika wata iskã a kansu da waɗansu rundunõni waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Yã kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa.
10. A lõkacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lõkacin da gannai suka karkata kuma zukãta suka kai ga maƙõsai, kuma kuka yi zaton zace- zace, game da Allah.
11. A can aka jarrabi mũminai, kuma aka yi girgiza da su, girgiza mai tsanani.
12. Kuma a lõkacin da munafukai da waɗanda akwai cũta a cikin zukãtansu ke cẽwa, Allah da ManzonSa, « Ba su yi mana wa'adin kõme ba, fãce rũɗi. »
13. Kuma a lõkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, « Ya mutãnen Yasriba! ( 1 ) Bã ku da wani matsayi, sabõda haka ku kõma. » Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman izni ga Annabi sunãcẽwa, « Lalle gidãjenmu kuranye suke, » alhãli kuwa bã kuranye suke ba, bã su da nufin kome fãce gudu.
14. Kuma dã an shige ta ( Madĩna ) a kansu, daga sasanninta, sa'an nan aka tambaye su fitina ( kãfirci ) , lalle dã sun jẽ mata, kuma dã ba su zauna a cikinta ( Madĩna ) ba fãce kaɗan.
15. Kuma lalle haƙĩƙa, sun kasance sunã yi wa Allah alkawari, a gabãnin wannan; Bã zã su jũya dõmin gudu ba, kuma alkawarin Allah ya kasance abin tambaya.
( 1 ) Sun kõma ga sũnan Madĩnan a zãmanin Jãhiliyya sunã izgili da cẽwa ba su yarda da sãbon sũnan ba na Madĩna, fãce Yasriba, sũnanta da suka sani na asali.