Hausa translation of the meaning Page No 418

Quran in Hausa Language - Page no 418 418

Suratul Al-Ahzab from 1 to 6


Sũratul Aḥzãb
Tanã karantar da yadda ake kashe miyãgun al’ãdun Jãhiliyya da ba Su dãce da Musulunci ba, da musanyar waɗanda suka dãce da sharĩ’a.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Yã kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai da munãfukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima.
2. Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa.
3. Ka dõgara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakĩli.
4. Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai.
5. Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan'uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma ( akwai laifi ) ga abin da zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
6. Annabi ne mafi cancanta ( 1 ) ga mũminai bisa ga su kansu, kuma mãtansa uwãyensu ne. Kuma ma'abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littãfin Allah bisa ga mũminai da Muhãjirai, fãce fa idan kun aikata wani alhẽri zuwa ga majiɓintanku. Wancan yã kasance a cikin Littafi, rubũtacce.
( 1 ) Idan son mũmini ya Sãɓãwa faɗar Annabi, sai ya bar son ransa ya kõma wa faɗar Annabi.