Hausa translation of the meaning Page No 43

Quran in Hausa Language - Page no 43 43

Suratul Al-Baqarah from 257 to 259


257. Allah Shi ne Masõyin waɗanda suka yi ĩmãni; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kãfirta, masõyansu Ɗãgũtu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.
258. Shin, ba ka gani ( 1 ) ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin ( al'amarin ) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: « Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa. » Ya ce: « Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa. » Ibrãhĩm ya ce: « To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma. » Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
259. Kõ kuwa ( 2 ) wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: « Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta. » Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: « Nawa ka zauna? » Ya ce: « Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini. » Ya ce: « A'a kã zauna shẽkara ɗari. » To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, ( kõwanensu ) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma « , To, a lõkacin da ( abin ) ya bayyana a gare shi, ya ce: » Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne. « »
( 1 ) Ƙissar farko ta Ibrãhĩm da Namarũzu.
( 2 ) Ƙissa ta biyu Uzairu da alƙarya matacciya, da jãkinsa, da abincinsa bãyan shẽkara ɗari.