Hausa translation of the meaning Page No 431

Quran in Hausa Language - Page no 431 431

Suratul Saba from 23 to 31


23. « Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye ( 1 ) tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma, »
24. Ka ce: « Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa? » Ka ce: « Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya. »
25. Ka ce: « Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba. »
26. Ka ce: « Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani. »
27. Ka ce: « Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima. »
28. Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
29. Sunã cẽwa, « Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya? »
30. Ka ce: « Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta. »
31. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: « Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba ( na waɗansu littattafan sama ) . » Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana ( mabiya ) suke cẽwa makangara ( shũgabanni ) « Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai. »
( 1 ) Bãbu wanda ya san lõkacin bãyar da izni ga yin cẽto kõwanda zã a bai wa iznin ya yi, kõ a yi masa, Sabõda haka mutãne a Lãhira na a cikin tsõro har a lõkacin da aka kuranye tsõron ta hanyar bãyar da izni ga cẽto babba ga Annabi Muhammadu, sai mũminai su yi farin ciki su dinga tambayar jũna da cẽwa, « Mẽnene Ubangijinku Ya ce? » waɗansu su ce, « Yã faɗi gaskiya' Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma. »