Hausa translation of the meaning Page No 432

Quran in Hausa Language - Page no 432 432

Suratul Saba from 32 to 39


32. Makangara suka ce wa maraunana, « Ashe, mũ ne muka kange ku daga shiriya a bãyan ya zo muku? Ã,a' kun dai kasance mãsu laifi. »
33. Kuma maraunana suka ce wa makangara. « Ã'a, ( ku tuna ) mãkircin dare da na rãna a lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan tãrayya. » Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
34. Kuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya fãce mani'imtanta ( shũgabanni ) sunce, « Lalle mũ, mãsu kãfirta ne da abin da aka aiko ku da shi. »
35. Kuma suka ce: « Mũ ne mafiya yawa ga dũkiya da ɗiya, kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba. »
36. Ka ce: « Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfiɗa arziki ga wanda Ya so, kuma Yanã ƙuntatãwa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. »
37. Kuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙãmi fãce wanda, ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan sunã da sakamakon ninkawa sabõda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin bẽnãye.
38. Kuma waɗanda suke mãkirci a cikin ãyõyinMu, sunã nẽman gajiyarwa, waɗannan abin halartãwa ne a cikin azãba.
39. Ka ce: « Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa, kuma Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa. »