Hausa translation of the meaning Page No 438

Quran in Hausa Language - Page no 438 438

Suratul Al-Fatir from 31 to 38


31. Kuma abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, daga Littãfi, shi ne gaskiya, mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi. Lalle ne Allah ga bãyinSa, haƙĩƙa, Mai labartawa ne, Mai gani.
32. Sa'an nan Mun gãdar da Littãfin, ga waɗanda Muka zãɓa daga bãyinMu, sa'an nan daga cikinsu, akwai mai zãlunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsakaitãwa, kuma daga cikinsu akwai mai tsẽrẽwa da ayyukan alhẽri da iznin Allah. Waccan ita ce falalar ( Allah ) mai girma.
33. Gidãjen Aljannar zamã sunã shigar su. Anã ƙawãce su a cikinsu, da ƙawã ta mundãye daga zĩnãriya da lu'ulu'u, kuma tufãfinsu, a cikinsu alharĩni ne.
34. Kuma suka ce: « Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tafiyar da baƙin ciki daga gare mu. Lalle Ubangijinmu, haƙĩƙa Mai gafarane, Mai godiya. »
35. « Wanda Ya saukar da mu a gidan zamã, daga falalarSa, wata wahala bã ta shãfar mu a cikinsa, kuma wata kãsãwa bã ta shãfar mu a cikinsa. »
36. Kuma waɗanda suka kãfirta sunã da wutar Jahannama, bã a yin hukunci a kansu balle su mutu kuma bã a sauƙaƙa musu daga azãbarta. Kamar haka Muke sãka wa kõwane mai yawan kãfirci.
37. Kuma sũ, sunã hargõwar nẽman ãgaji a cikinta. ( Sunã cẽwa ) « Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance munã aikatãwa. » Ashe, kuma, ba Mu rãyar da ku ba, abin da mai tunãni zai iya yin tunãni a ciki, kuma mai gargaɗi yã jẽ muku? To, ku ɗanɗana, sabõda haka bãbu wani mataimaki, ga azzãlumai.
38. Lalle Allah ne Masanin gaibin sammai da ƙasã. Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake ainihin zukata.
( 1 ) ( 1 ) Littattafan sama a gabãnin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi.
( 2 ) ( 2 ) Alƙur'ãni.