Hausa translation of the meaning Page No 437

Quran in Hausa Language - Page no 437 437

Suratul Al-Fatir from 19 to 30


19. Kuma makãho bã ya daidaita da mai gani.
20. Kuma duffai bã su daidaita, kuma haske bã ya daidaita.
21. Kuma inuwa bã ta daidaita, kuma iskar zãfi bã ta daidaita.
22. Kuma rãyayyu bã su daidaita kuma matattu ba su daidaita. Lalle Allah Yanã jiyar da wa'azi ga wanda Ya so, kuma ba ka jiyar da waɗanda suke a cikin kaburbura.
23. Ba ka zama ba fãce mai gargaɗi kawai.
24. Lalle Mũ Mun aike ka da gaskiya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Kuma bãbu wata al'umma fãce wani mai gargaɗi yã shũɗe a cikinta.
25. Kuma idan sunã ƙaryata ka, to, haƙĩƙa, waɗanda suke a gabãninsu sun ƙaryata. Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske.
26. Sa'an nan Na kãma waɗanda suka kãfirta. To, yãya musũNa yake?
27. Ba ka gani ba, lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama? Sai Muka fitar, game da shi,'yã'yan itãce mãsu sãɓanin launuka kuma daga duwatsu akwai zane- zane, farfaru da jãjãye, mãsu sãɓanin launin, da mãsu launin baƙin ƙarfe, baƙãƙe.
28. Kuma daga mutãne da dabbõbi da bisãshen gida, mãsu sãɓãnin launinsu kamar wancan. Malamai kawai ke tsõron Allah daga cikin bãyinSa. Lalle, Allah, Mabuwãyi ne, Mai gãfara.
29. Lalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah ( 1 ) kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan ( sãmun ) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro.
30. Dõmin ( Allah ) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙarã musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gãfara ne, Mai gõdiya.
( 1 ) Littattafan sama a gabãnin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi.