Hausa translation of the meaning Page No 451

Quran in Hausa Language - Page no 451 451

Suratul Al-Saffat from 127 to 153


127. Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne ( a wutã ) .
128. Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
129. Kuma Muka bar ( yabo ) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
130. Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
131. Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
132. Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
133. Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
134. A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
135. Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa ( a cikin azãba ) .
136. Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
137. Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
138. Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
139. Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
140. A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
141. Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
142. Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
143. To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
144. Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
145. Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
146. Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
147. Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa ( a kan haka ) .
148. Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
149. Sabõda haka, ka tambaye su, « Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza? »
150. Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
151. To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.
152. « Allah Yã haihu, » alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
153. Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?