Hausa translation of the meaning Page No 452

Quran in Hausa Language - Page no 452 452

Suratul Al-Saffat from 154 to 182


154. Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa ( wannanhukunci ) ?
155. Shin, bã ku tunãni?
156. Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
157. To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
158. Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, « Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne ( a cikin wutã. ) »
159. Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
160. Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
161. To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
162. Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
163. Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
164. « Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, ( 1 ) fãce yanã da matsayi sananne. »
165. « Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu- sahu ( dõmin ibãda ) . »
166. « Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi. »
167. Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
168. « Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko. »
169. « Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. »
170. Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
171. Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
172. Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
173. Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
174. Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
175. Ka nũna musu ( gaskiya ) , da haka zã su dinga gani. ( 2 )
176. Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
177. To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
178. Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
179. Ka nũna ( musu gaskiya ) , da haka zã su dinga nũnãwa.
180. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
181. Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
182. Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
( 1 ) Malã'iku da sauran halitta duka kõwa yã san matsayinsa na bauta ga Allah wanda ba Ya da dã ko diya, kuma ba Ya da dangantaka da kõwa.
( 2 ) Wannan ƙãrin bayãni ne ga abin da sũrar ke karantarwa na cewa Annabãwa sũ ne kamar rãna mai haske na asali. Mãlamai kamar taurãri suke mãsu sãmun haske daga rana su wãtsa ga dũniya kuma su kõre ɓarna. Aya ta l79 da ke tafe karfafawa ce ga ma'anar wannan.