Hausa translation of the meaning Page No 450

Quran in Hausa Language - Page no 450 450

Suratul Al-Saffat from 103 to 126


103. To, a lõkacin da suka yi sallama, ( Ibrahĩm ) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.
104. Kuma Muka kira shi cẽwa « Ya Ibrahĩm! »
105. « Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin. » Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
106. Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
107. Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
108. Kuma Muka bar ( yabo ) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
109. Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
110. Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
111. Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
112. Kuma Muka yi masa bushãra ( 1 ) Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
113. Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa ( ga zãluncin ) .
114. Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.
115. Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
116. Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
117. Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
118. Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
119. Kuma Muka bar ( yabo ) a gare su a cikin mutãnen karshe.
120. Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
121. Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
122. Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai.
123. Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
124. A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, « Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba? »
125. « Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta? »
126. « Allah Ubangijinku,kuma Ubangijin ubanninku farko? »
( 1 ) Wannan sãbuwar bushãra da Is'hãƙa tanã nũna cẽwa bã shĩ ne wanda kissar yankã ta shãfa ba sabõda haka Isma'ĩla dai ne tabbas, mai ƙissar yankã. Sabõda haka Allah Ya sanya shi wata al'umma dabam' dõmin a sãka masa, sa'an nan akasãka wa Ibrãhĩm da Is'hãƙa dõmin ya zama wata al'umma ta dabam,