Hausa translation of the meaning Page No 47

Quran in Hausa Language - Page no 47 47

Suratul Al-Baqarah from 275 to 281


275. Wadanda suke cin ribã ( 1 ) ba su tashi, fãce kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: « Ciniki kamar riba yake. » Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa ( ana wakkala shi ) zuwa ga Allah.Kuma wanda ya kõma,to,waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.
276. Allah Yana shãfe albarkar riba, kuma Yana ƙãra sadakõki. Kuma Allah bã Ya son dukan mai yawan kãfirci, mai zunubi.
277. Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.
278. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance mãsu ĩmãni.
279. To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yãƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tũba to kuna da asalin dũkiyõyinku, bã ku zãlunta, kuma bã a zãluntar ku.
280. Kuma idan ma'abucin wahala ya kasance ( mawahalci ) to, jinkirtãwa ake yi zuwa ga sauƙin al'amarinsa, kuma dã kun yi sadaka, shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kuna sani.
281. Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su.
( 1 ) Ribã ita ce ƙãri ga adadi koga lõkaci. Amma ƙãrin adadi shi ne ƙãri a cikin mu'ãmala da zinãri da azurfa da abũbuwan ci ga rayuwa. Yana haramta ga jinsi guda kawai, kuma ana sharɗantawa ga abinci ya zama abinci kõ abin gyaransa, kuma anã iya aijiye shi, ban da 'ya'yan itãcen marmari da duma da ruwa. Amma ga jinkiri an hana riba baki ɗaya. kõ dã ga 'ya'yan itãcen marmari. Takardun kuɗi kamar sil'õ'i suke dõmin haka ƙimarsu tana hawakuma tanã sauka. Har yanzu malamai ba su yanke hukunci a kansu ba sõsai. Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: « Ka barabin da yake sanya maka shakka zuwa ga wanda ba ya sanya maka shakka. »