Hausa translation of the meaning Page No 46

Quran in Hausa Language - Page no 46 46

Suratul Al-Baqarah from 270 to 274


270. Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, kõ kuka cika alwãshi daga wani bãkance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzãlumai bã su da wasu mataimaka.
271. Idan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.
272. Shiryar da su bã ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, dõmin kanku ne, kuma bã ku ciyarwa, fãce dõmin nẽman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alhẽri zã a cika lãdarsa zuwa gare ku, alhãli kuwa kũ bã a zãluntarku.
273. ( Ciyarwar a yĩ ta ) ga matalautan ( 1 ) nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne.
274. Waɗanda suke ciyar da dukiyõyinsu, a dare da yini, ɓõye da bayyane, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu. Kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.
( 1 ) Matalautan nan 'muhãjiruna'ne waɗanda suka bar dũkiyarsu da iyãlansu dõmin hijira. Kuma ba su sãmi wata matãka ba a Madĩna, sai aka yimusu rumfuna, sunã kwãna a ciki, suka tsare kansu dõmin jihãdi da yãƙi da karãtun Alƙur'ãni da ibãda kamar matsayin sõja a yanzu. Sũ wajen ɗari huɗu ne, shugabansu, shi ne Abdur Rahmanbn Sakhar Abu Huraira el Dawsy.