Surah Fussilat | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 477
Suratul Fussilat from 1 to 11
Sũratu Fuṣṣilat
Tanã karantar da mutãne cẽwa hãlayensu duka cũta ne, Alkur’ãni ne mãganin wannan cũtar.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ḥ. M̃.
2. Saukarwa ( da Alƙur' ãni ) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai.
3. Littãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki- daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani
4. Yanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Sai mafi yawansu suka bijire. Sabõda haka sũ, bã su saurãrãwa.
5. Kuma suka ce: « Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne. »
6. Ka ce: « Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi gafararSa. » Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki.
7. Waɗanda bã su bãyar da zakka, kuma sũ a game da Lãhira su kafirai ne.
8. Lalle wɗdanda suka yi ĩmãni, Kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bai yankẽwa.
9. Ka ce: « Ashe lalle kũ, haƙĩƙa, kunã kafurta a game da wanda Ya halitta kasã a cikin kwanuka biyu, kuma kunã sanya Masa kĩshiyõyi? Wancan fa, shĩ ne Ubangijin halittu. »
10. Kuma Ya sanya, a cikinta, dũwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, kuma Ya ƙaddara abũbuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu mãsu daidaita, dõmin matambaya.
11. Sa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita ( a lõkacin ) hayãƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasã « Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas. » Suka ce: « Mun zo, munã mãsu ɗã'ã. »