Hausa translation of the meaning Page No 490

Quran in Hausa Language - Page no 490 490

Suratul Zukhruf from 11 to 22


11. Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku ( daga kabari ) .
12. Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa.
13. Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, « Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba. »
14. « Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu ( 1 ) jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu. »
15. Kuma suka sanya ( 2 ) Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin.
16. Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza?
17. Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki.
18. Ashe, kuma ( Allah zai zãɓi ) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba?
19. Kuma suka mayar da malã'iku ( 'yã'ya ) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin ( Allah ) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su.
20. Kuma suka ce: « Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba. » Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki- faɗi.
21. Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa ( Alƙur'ãni ) sabõda haka da shĩ suke riƙe?
22. Ã'a, sun ce dai, « Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini ( na al'ãda ) kuma lalle mũ, a kan gurãbunsu muke mãsu nẽman shiryuwa. »
( 1 ) Ku yi dalĩli da hõrẽwar abinhawa gare ku zuwa ga tabbatar tãshinku dõmin hisãbin Ƙiyãma, dõmin ku bi umurninsa a dũniya, kuma ku bar al'adunku.
( 2 ) suka ce malã'iku 'ya'ya mãtane na Allah, sunã bauta musu ne dõmin su kusantar da su zuwa ga Allah, watau dõmin su cẽce su daga azãba. Sun yi wannan ƙarya ne dõmin su tabbatar da al'ãdarsu ta surkulle. Sabõda haka suka yi wa Allah ƙarya suka naƙasa shi da haka, kuma suka naƙasa malã'iku mãsu daraja a wurin Allah kuma suka kãfirce wa ni'imar da Allah Ya yi musu wajen aiko musu Manzo mai shiryar da su. Sa'an suka kafa hujja da ƙarya dõmin su danne gaskiya.