Surah Az-Zukhruf | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 491
Suratul Zukhruf from 23 to 33
23. Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, « Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbunsu. »
24. ( Sai mai gargaɗin ) ya ce: « Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba? » Suka ce, « Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi. »
25. Sabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take.
26. Kuma ( ka ambaci ) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, « Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa. »
27. « Fãce wannan ( 1 ) da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni. »
28. Kuma ( Ibrãhĩm ) ya sanya ( ita wannan magana ) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata.
29. Ã'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu.
30. Kuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: « Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne. »
31. Kuma suka ce: « Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun ( 2 ) nan biyu ba? »
32. Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka ( ta Annabci ( 3 ) ) , ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa.
33. Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa.
( 1 ) Bã ni bauta wa gumãka, amma inã bauta wa Allah wanda Ya ƙãga halittata.
( 2 ) Sunã nufin Makka da tã'ifa, kuma sunã nufi a saukar da Alƙur'ãni ga walĩduɗan Mugĩra na Makka kõ ga Urwatu ɗan Mas'ũdi As saƙafi a Ta'ifa. Watau sunã sũkar Muhammadu dõmin bã shi dadũkiya. A gare su mai dũkiya shĩ ne babban mutum, wanda ya cancanta Allah Ya aiko shi ga mutãne.
( 3 ) Tun da ba Mu bar rabon abincin rãyuwarsu ta dũniya a hannunsu ba, to, ta yãya ne zã Mu bar babban abu kamar Annabci da shiryar da mutãne ga hannãyensu? Wãtau bã zai yiwu Mu yi ba sai yadda Muke so kawai, kõ su bi, kõ su kãfirta, duka daidai ne a gare Mu.