Surah Ad-Dukhan | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 497
Suratul Al-Dukhan from 19 to 39
19. « Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne. »
20. « Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni. »
21. « Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni. »
22. Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.
23. ( Allah Ya ce ) : « To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne ( dõmin a kãma ku. ) »
24. « Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa. »
25. Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.
26. Da shuke- shuke da matsayi mai kyau.
27. Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.
28. Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.
29. Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka ( 1 ) a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
30. Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.
31. Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.
32. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi ( na Taurata ) a kan mutãne.
33. Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna ( 2 )
34. Lalle waɗannan mutãne ( 3 ) , haƙĩka, sunã cẽwa,
35. « Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba. »
36. « Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya. »
37. shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.
38. Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.
39. Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.
( 1 ) Watau sama da ƙasa ba su girgizu ba sabõda halaka su da aka yi kamar ba a yi, kõme ba.
( 2 ) An bai wa Banĩ lsrã'ĩla ni'imar ilmi na Taurãta, an ɗaukaka su, sabõda aiki da ilmin, a kan sauran mutãnen zãmaninsu, kuma aka bã su ãyõyin mu'ujiza kamar tsãge tẽku da mannu da salwa da sauransu, amma kuma dukkan waɗannan ni'imomĩn sai da suka gushe a lõkacin da suka sãɓa wa umurnin Allah, sai kumaƙasƙanci ya maye musu daga bãya. Wannan kuma wa'azi ne ga Musulmi waɗanda Allah Ya ɗaukaka su da Alƙur'ãni a kan sauran mutãne, idan sun kauce masa zã su walãkantu.
( 3 ) Anã nufin mutãnen zãmanin Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, waɗanda ake kiran su zuwa ga Musulunci.