Hausa translation of the meaning Page No 498

Quran in Hausa Language - Page no 498 498

Suratul Al-Dukhan from 40 to 59


40. Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.
41. Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.
42. fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi ( Allah ) , shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
43. Lalle itãciyar zaƙƙũm ( ɗanyen wutã ) ,
44. Ita ce abincin mai laifi.
45. Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.
46. Kamar tafasar ruwan zãfi.
47. ( A cẽ wa malã'ikun wutã ) , « Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm. »
48. « Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi. »
49. ( A ce masã ) , « Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma! »
50. « Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi. »
51. Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.
52. A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.
53. Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.
54. Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.
55. Sunã kira, a cikinsu ( gidẽjen ) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu ( daga dukan abin tsõro ) .
56. Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma ( Allah ) , Ya tsare musu azãbar Jahĩm.
57. Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
58. Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi ( Alƙur'ãni ) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.
59. Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne. ( 1 )
( 1 ) Mãsu jira ne ga abin da zai sãme su idan ba su yi ĩmãni ba, watau ni'imar da aka ba su zã ta gushe ke nan dõminba su aiwatar da ita ba a kan umuruin Allah.