Hausa translation of the meaning Page No 496

Quran in Hausa Language - Page no 496 496

Suratul Al-Dukhan from 1 to 18


Sũratud Dukhãn
Tanã karantar da cẽwa Allah Yanã tadbĩri ga al’amuranSa kãfin Ya bayyana su ga bayinSa. Kuma ni’imarSa tanã gushẽwa sabõda sãɓã wa umurninSa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ḥ. M̃.
2. Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
3. Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.
4. A cikinsa ( shi daren ) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.
5. Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.
6. Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.
7. ( Shĩ ne ) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni ( za ku gãne haka ) .
8. Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. ( Shi ne ) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
9. A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.
10. Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.
11. Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.
12. Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.
13. Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu ( da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba ) ?
14. Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: « Wanda ake gayãwa ( 1 ) ne, mahaukaci. »
15. Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne ( ga laifin ) .
16. Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.
17. Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.
18. ( Mazon ya ce ) : « Ku kãwo mini ( ĩmãninku ) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku. »
( 1 ) Sunã nufin waɗansu mutãne ne ke gaya wa Annabi Alƙur'ãni, kõ kuma daga alãma watau wai Annabi taɓaɓɓe ne, mahaukaci. Taɓaɓɓe da mahaukaci duka ma'anarsu guda ce, watau marashin hankali,wanda aka yi wa alãma da rashin hankali.