Hausa translation of the meaning Page No 504

Quran in Hausa Language - Page no 504 504

Suratul Al-Ahqaf from 15 to 20


15. Kuma Mun yi wasiyya ga mutum ( 1 ) game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in,ya ce: « Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa ( ga umurninKa ) . »
16. Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Muke gãfarta mafi mũnanan ayyukansum ( sunã ) a cikin 'yan Aljanna, a kan wa'adin gaskiya wanda suka kasance anã yi musu alkawari ( da shi ) .
17. Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: « Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga ( kabari ) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna ( ba su kõmo ba ) ? » Kuma sũ ( mahaifan ) sunã nẽman Allah taimako ( sunãce masa ) « Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. » Sai shi kuma ya ce. « Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko. »
18. Waɗancan ne waɗanda kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin al'ummõmi waɗanda suka shũɗe, ( bã da daɗẽwa ba ) , a gabãninsu, daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra.
19. Kuma ga kõwane nau'i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin ( Allah ) Ya cika musu ( sakamakon ) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su ba.
20. Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã ( a ce musu ) : « Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi. »
( 1 ) Mutum a cikin iyãlinsa, kõ ya zama mai gargaɗi ga kansa da nasĩha ga mahaifansa da zuriyarsa kamar yadda ya bayyana a cikin ãyõyi 13,l4 da l5, kõ kuma ya zama mai butulci ga kansa, ya tõzartar da iyãyensa da zuriyarsa, kamar yadda ya bayyanaa cikin ãyõyi 17 da 18.