Hausa translation of the meaning Page No 503

Quran in Hausa Language - Page no 503 503

Suratul Al-Ahqaf from 6 to 14


6. Kuma idan aka tãra mutãne sai su kasance maƙiya a gare su, alhãli sun kasance mãsu ƙi ga ibãdarsu.
7. Kuma idan anã karãtun ãyõ?yinMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta ga gaskiya a lõkacin da ta jẽ musu, su ce, « Wannan sihiri ne bayyananne. »
8. Kõkuwã sunã cẽwa: « Yã ƙirƙira shi ( Alƙur'ãni ) ne? » Ka ce: « Idan na ƙirƙira shi ne, to bã ku mallaka mini kõme daga Allah. Shĩ ne Mafi sani ga abin da kuke kũtsãwa a cikinsa na magana. ( Allah ) Yã isa Ya zama shaida a tsakãnĩnada tsakãninku. Kuma shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. »
9. Ka ce: « Ban kasance fãrau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da zã a yi game da ni kõ game da ku ( na gaibi ) ba, bã ni bin kõme fãce abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban zama ba, fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa. »
10. Ka ce: « Shin, kun gani, idan ( Alƙur'ãni ) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kãfirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banĩ Isrã'ĩla ya bãyar da shaida a kan kwatankwacinsa, sa'an nan ya yi ĩmãni, kuma kuka kangare? Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. »
11. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: « Da ( Alƙur'ãni ) ya kasance, wani alhẽri ne, » dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, « Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe. »
12. Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan ( Alƙur'ãni ) littafi ne mai gaskatãwa ( ga littafin Mũsã ) , a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa.
13. Lalle ne waɗanda ( 1 ) suka ce: « Ubangijinmu Allah ne, » sa'an nan suka daidaitu, to, bãbu wani tsõro a kansu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba.
14. Waɗannan 'yan Aljanna ne, sunã madawwama a cikinta, a kan sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
( 1 ) Yã fara da wanda ya yi wa kansa nasĩha, kuma ya yi aiki da ita, to, shĩ mai gargaɗi ne. Haka kuma mai yin nasĩha ga mutãne, shĩ mã mai gargaɗi ne.