Hausa translation of the meaning Page No 505

Quran in Hausa Language - Page no 505 505

Suratul Al-Ahqaf from 21 to 28


21. Kuma ka ambaci ɗan'uwan ( 1 ) Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi ( da cẽwa ) « Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma. »
22. Suka ce: « Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya. »
23. Ya ce: « Ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma inã iyar maku abin da aka aiko ni da shi, kuma amma inã ganin, kũ, wasu mutãne ne, kunã jãhiltar gaskiya. »
24. To, a lõkacin da suka ga azãbar, kumar hadari mai fuskantar rãfukansu, suka ce: « Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. Ã'a, shĩ na abin da kuke nẽman gaggawar saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi. »
25. Tanã darkake kõwane abu da umurnin Ubangijinta. Sai suka wãyi gari, bã a ganin kõme fãce gidãjensu. Kamar wannan ne Muke sãka wa mutãne mãsu laifi.
26. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba, kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya wajaba ( 2 ) a gare su.
27. Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo.
28. To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi.wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba ? Ã'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa.
( 1 ) Ya ambaci hũdu da mutãnensa Ãdãwa da misãlinwaɗansu mãsu garagɗi daga Annabãwan da suka shũɗe da kuma mutãnensu da yadda aka halaka su daga inda suke zaton rahama ta Jẽ musu. Haka ne hukuncin. Dukan wanda aka yi wa gargaɗi da bin umurnin Allah, idan ya ƙi bi, sa'an nan ya bi son zũciyarsa, Allah zai. Kãwo masa azãba daga inda yake zaton alhẽri ga kansa.
( 2 ) Ya wajaba a gare su, watau sakamakonsa ya tabbata a kansu da azãba.