Hausa translation of the meaning Page No 506

Quran in Hausa Language - Page no 506 506

Suratul Al-Ahqaf from 29 to 35


29. Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu ( 1 ) zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: « Ku yi shiru. » Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi.
30. Suka ce: « Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn Mũsã,mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya. »
31. « Yã mutãnenmu! Ku karɓa wa mai kiran Allah, kuma ku yi ĩmãni da Shi, Ya gãfarta muku daga zunubanku, kuma ya tserar da ku daga azãba mai raɗaɗi. »
32. « Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwãya a cikin ƙasa ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan sunã a cikin ɓata bayyananna. »
33. Shin, kuma ba su gani ba cẽwa: « Lalle Allah, Wanda Yã halitta sammai da ƙasa kuma bai kãsa ga halittarsu ba, Mai ĩkon yi ne a kan rãyar da matattu? » Na'am, lalle Shi, Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
34. Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, ( a ce musu ) « Ashe, wannan bã gaskiya ba ne? » Su ce: « Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu! » Sai Ya ce, « To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci. »
35. Sabõda haka, ka yi haƙuri kamar yadda mãsu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggãwa. Kamar dai sũ, a rãnar da suke ganin ( sakamako ) abin da ake yi musu wa'adi ba su zauna ba, fãce sa'a guda daga yini. Iyarwa dai da Manzanci
) . Shin, akwai wanda za a halakar? ( Bãbu ) , fãce mutãne fasiƙai.
( 1 ) Wannan yã nũna cẽwa a cikin aljannu akwai Musulmi da masu gargaɗi, kuma idan mutum ya yi gargaɗi, dõmin Allah, Allah zai taimake shi da mãsu saurãra masa, kõ da daga waɗansu jinsin da ba nãsa ba. Kuma zama a cikin wani addinin Allah da ya shige, ba ya isa ga wanda bai shiga addinin Musulunci ba, a bãyan bayyanar Musulunci.