Hausa translation of the meaning Page No 507

Quran in Hausa Language - Page no 507 507

Suratul Muhammad from 1 to 11


Sũratu Muḥammad
Tanã karantar da kwaɗaitarwa ga yin jihãdi dõmin tsarona ddini da takõbi, kuma tanã gargaɗi ga barin jihãɗi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange mutãne daga tafarkin Allah, ( Allah ) Ya ɓatar da ayyukansu.
2. Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, ( Allah ) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu.
3. Wannan kuwa sabõda lalle, waɗanda suka kãfirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda suka yi ĩmãni, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana wa mutãne misãlansu.
4. Sabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi. Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu ( ba tare da yaƙin ba ) kuma amma ( ya wajabta jihadi ) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah, ( 1 ) to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba.
5. Zai shiryar da su, kuma Ya kyautata hãlãyensu.
6. Kuma Ya shigarda su Aljanna ( wadda ) Ya siffanta ta a gare su.
7. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku. ( 2 ) .
8. Kuma waɗanda suka kãfirta, to, ruɓushi ya tabbata a gare su, kuma ( Allah ) Ya ɓatar da ayyukansu.
9. Wannan, sabõda lalle sũ, sun ƙi abin da Allah Ya saukar dõmin haka Ya ɓata ayyukansu.
10. Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai ( na kõwane zãmani ) .
11. Wancan! Sabõda lalle Allah ne Majiɓincin waɗanda suka yi ĩmãni, kuma lalle, kafirai bãbu wani majiɓinci a gare su.
( 1 ) Tafarkin Allah, ( fi sabilillahi ) a wannan sũra tanã nufin jihãdi na takõbi dõmin ɗaukaka kalmar Allah da tsare ta. Anã fassara tafarkin Allah a waɗansu wurãre da jihãdi na takõbi kõ na magana dõmin shiryar da mutãne kõ dõmin tsaron gaskiya, kõ kuma karantarwa, da kuma tsare rai daga sha'awarta da hushinta. A cikin Hadisi anã ruwaitõwa cẽwa tsaron rai daga sha'awarta da hushinta shĩ ne jihãdiwanda ya fi girma.
( 2 ) Tabbatar da dugadugan ƙafãun, yanã nufin sanya musu zãrumci a cikin zukãtansu, dõmin ƙafãfunsu, su kafu a wurin yaƙi, dõmin kada su gudu.