Hausa translation of the meaning Page No 508

Quran in Hausa Language - Page no 508 508

Suratul Muhammad from 12 to 19


12. Lalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi ( adũniya ) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su.
13. Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su.
14. Shin, wanda ya kasance a kan wata hujja daga Ubangijinsa, zai zama kamar wanda aka ƙawãce masa mugun aikinsa, kuma suka bibbiyi son zũciyõyinsu?
15. Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. ( Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita ) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu?
16. Kuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare ( 1 ) zuwa gare ka, har idan sun fita daga wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi « Mẽne ne ( Muhammadu ) ya fãɗa ɗazu? » Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shãfe haske daga zukãtansu, kuma suka bi son zũciyõyinsu.
17. Kuma waɗannan da suka nẽmi shiryuwa ( Allah ) Ya ƙara musu shiryuwarsu, kuma Yã bã su ( sakamakon ) taƙawarsu. ( 2 )
18. To shin sunã jiran ( wani abu ) ? Fãce S'a ta jẽ musu bisa abke, dõmin lalle sharuɗɗanta sun zo. To, yãya tunãwarsu ( 3 ) take, idan har ta jẽ musu?
19. Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka, ( 4 ) ( kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.
( 1 ) Wannan shĩ ya nũna cẽwa wani ɗan rahõto ba zai iya fahimtar gaskiya ba, matuƙar anã aikin Allah da gaskiya. Allah na sanya trõro a cikin zukãtan kãfirai.
( 2 ) Taƙawa, ita ce bin umuruin Allah da nĩsantar haninsa sabõada haka abin da Allah ke bai wa mai taƙawa, shi ne sakamkon aikinsa wanda ya yi daidai da sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare Shi.
( 3 ) Tunãwarsu da wa'aztuwarsu ga Sa'a bã zai yi musu amfãni ba, a bãyan tã je musu. Wa'azi bã ya amfãni, sai idan wanda aka yi wa shi, yã yi aikida shi a gabãnin mutuwa ta jẽ masa.
( 4 ) An umurci Annabi ya nẽmi gãfara dõmin mutãne su yi kõyi da shi, dõmin Allah Ya riga ya tsare shi daga zunubia gabãni da bayan Manzanci.