Hausa translation of the meaning Page No 509

Quran in Hausa Language - Page no 509 509

Suratul Muhammad from 20 to 29


20. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: « Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? » To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su:
21. Yin ɗã'a da magana mai kyau. Sa'an nan idan al'marin ya ƙullu, ( 1 ) to, dã sun yi wa Allah gaskiya, lalle dã ya kasance mafifi ci a gare su.
22. To, shin, kunã fãtan idan kun jũya ( daga umurnin ) zã ku yi ɓarna a cikin ƙasã, kuma ku yan yanke ( 2 ) zumuntarku?
23. Waɗannan sũ ne waɗanda Allah Ya la'anẽ su, sa'an nan Ya kurumtar da su, kuma Ya makantar da ganinsu.
24. Shin to, bã zã su, kula da Alƙur'ãni ba, kõ kuwa a bin zukã tansu akwai makullansu?
25. lalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su, Shaiɗan ne ya ƙawãta ( 3 ) musu ( haka ) , kuma ya yi musu shibta.
26. Wancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: « Za mu yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin, » alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta asĩri.
27. To, yãya hãlinsu yake a lõkacin da malã'iku ke karɓar rãyukansu, sunã dũkan fuskõkinsu da ɗuwaiwansu?
28. Wannan, dõmin lalle sũ sun bi abin da ya, fusãtar da Allah kuma sun ƙi yardarSa, sabõda haka Ya ɓãta ayyukansu.
29. Ko kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle- ƙullen su ( ga Musulunci ) ba?
( 1 ) kulluwar a'lamari, shĩ ne umurni da yin yãƙi, yi wa Allah gaskiya, shĩ ne zartar da umurninSa, bã tãre da tsõro ba. Tsõro, mũnafunci ne.
( 2 ) Dõmin barin jihãdi yanã kai ga wãtsuwar ɓarna da fasãdi a cikin ƙasã. Wãtsuwar fasãdi,yanã kai ga yanke zumunta tsakãnin dangi, sabõda zãluntar jũna.
( 3 ) Barin jihãdi, ridda ne da kõmãwa zuwa ga kãfirci da ƙawãtãwar Shaiɗan cẽwa rashin zuwa yãƙi na sanya kwanciyar hankali da rashin mutuwa, kuma yanã sanya musu waswasi da haka.