Hausa translation of the meaning Page No 514

Quran in Hausa Language - Page no 514 514

Suratul Al-Fath from 24 to 28


24. Kuma Shĩ ne Ya kange hannayensu ( 1 ) daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a cikin Makka, bãyan Ya rinjãyar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa.
25. Sũ ne waɗanda suka kãfirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya tanã tsare ( sun hana ta ) ta isa ga wurinta. Kuma bã dõmin waɗansu maza mũminai da waɗansu mãtã mũminai ba ba ku sansu ba ku tãkã su har wani aibi ya sãme ku daga gare su, bã da sani ba, ( dã Allah Yã yi muku iznin yãƙi ) , dõmin Allah Ya shigar da wanda Yake so a cikin rahamarSa. Da ( mũminai ) sun tsabbace dã Mun azabtar da waɗanda suka kãfirta daga gare su da azãba mai raɗiɗi.
26. A lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka sanya hanãnar ƙabĩ lanci a cikin zukãtansu hanãnar ƙabĩlanci irin ( 2 ) na Jãhiliyya sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa, kuma da a kan mũminai kuma Ya lazimta musu kalmar taƙawa ( 3 ) alhãli kuwa sun kasance mafi dãcẽwa da ita kuma ma'abutanta. Kuma Allah ya kasance Masani game da dukan kõme.
27. Lalle ne haƙĩƙa Allah Ya gaskata wa ManzonSa mafarkinsa da gaskiya: Lalle zã ku shiga Masallacin Harami, in Allah Ya so, kunã mãsu natsuwa, mãsu aske kawunanku da mãsu suisuye, bã ku jin tsõro, dõmin ( Allah ) Ya san abin da ba ku sani ba, sa'an nan Ya sanya wani cin nasara makusanci a bãyan wannan.
28. Shĩ ne wanda Ya aiki ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya dõmin Ya rinjãyar da shi a kan addinai dukansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai shaida.
( 1 ) Waɗansu Ƙuraishawa ne, sũ tamãnin, suka kẽwaye Musulmi a Hudaibiyya, da niyyar yaudara, sai aka kãme su, su duka, aka kai su ga Annabi, shi kuma ya yãfe musu, a bãyan ya nũna musu rinjãya. Wannan shĩ ne ya sabbaba yin sulhu.
( 2 ) A lõkacin da Ƙuraishi suka ga bã su iya yãƙi da Annabi, suka dõge da ƙabĩlancinsu, ta hanyar sulhu. Suka aika sahlu bn Amru da Huwaitib bn Abdul Uzza da Makraz bn Hafsbn Ahnaf dõmin nẽman sulhu bisa kada Annabi ya shiga Makka a wannan shẽkara, amma shẽkara mai kõmõwa ya jẽ ya shiga Makka kwana uku, su kuma su fita har ya ƙãre Umra ya fita. Annabi ya karɓi sulhun. Aka ce Aliyu bn Abi Talib ya rubũta. Wajen rubũtun kuma aka so a yi tãshinhankali, dõmin ya rũbuta, Manzon Allah ya yi sulhu da Ƙuraishãwa, sai kuma suka ce ba su yarda a rubũta kalmarManzon Allah ba. Sai Annabi ya sanya hannunsa mai daraja ya sõke kalmar da ake sãɓãni a kanta. Allah Ya saukar da natsuwa ga kõwa.
( 3 ) Kalmar taƙawa ita ce kalmar shahãda dõmin ɗaukar alkawari da ita yanã lazimtawa mai ita bin umurnin Allah da dãɗi kõ ba daɗi ta haka sai natsuwa ta sãmu. Anã ce mata kalmar taƙawa dõmin da ita ake kãre rai daga bin shaiɗan. Ma'anar taƙawa, ita ce kãriya.