Hausa translation of the meaning Page No 516

Quran in Hausa Language - Page no 516 516

Suratul Al-Hujurat from 5 to 11


5. Kuma dã lalle sũ, sun yi haƙuri har ka fita zuwa gare su, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri gare su, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
6. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi ( 1 ) Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.
7. Kuma ku sani ( cẽwa ) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga ( hãlãye ) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan ( da suka lazimci sifõfin nan ) su ne shiryayyu.
8. Bisa ga falala daga Allah da ni'ima. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
9. Kuma idan jama'a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita. ( 2 ) Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa.
10. Mũminai 'yan'uwan jũna kawai ne, sabõda haka ku yi sulhu a tsakãnin 'yan'uwanku biyu, kuma ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, a yi muku rahama.
11. « Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne ( abin yi wa izgilin ) su kasance mafifita daga gare su ( mãsu izgilin ) , kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ.Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai. »
( 1 ) Idan wani yã kai lãbãrin ɓarna, kada a yi aiki da shi sai bãyanan bincika an san gaskiyar al'amarin, kãfin a yi aiki da shi. fãsiƙi ga asalin kalma shi ne duka wanda ya karkace daga hanyar ƙwarai wadda aka sani. A nan, fãsiƙi, shi ne mai kai lãbãrin da yake akwai tãshin hankali a cikinsa, ko kuma abin tsõro dõmin ya sanya rũɗu a tsakãnin jama'a tun ba a san haƙĩƙanin al'amarin ba.
( 2 ) Wannan tsãri na sulhu a tsãkanin al'umma biyu mãsu faɗa, shĩ ne hanya mafi kyau wadda har yanzu wayon dũniya bai kai ga yin aiki da shi ba. Dã yanzu an zauna lãfiya, dã Majalisar Ɗinkin Dũniya na iya aiki da shi. haka Yake kuma ga sauran hukunce- hukuncen mutãnen dũniya. Shari'ar Musulunci sabõda ãdalcin da ke cikinta kuma wayon dũniya bai kai ta ga anã iya zartar da shi ba, shĩ ne ya sa ƙasãshen Musulunci ke kaucẽwa gare ta, dõmin son ran shugabanninsu. Allah Yã mayar da mu ga addininmu! Dukan Musulmin da ya kaucewa sharĩ'ar Musulunci, to, ya kauce ne dõmin ya sami damar yin zãlunci, kuma idan yã halatta kaucewar, yã zama bã Musulmi ba.