Hausa translation of the meaning Page No 524

Quran in Hausa Language - Page no 524 524

Suratul Al-Tur from 15 to 31


15. « To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani? »
16. « Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
17. Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.
18. Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.
19. ( A ce musu ) : « Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
20. Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.
21. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu ( 1 ) suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.
22. Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.
23. Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.
24. Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.
25. Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.
26. Suka ce: « Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan ( a dũniya ) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro. »
27. « To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi. »
28. « Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama. »
29. To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.
30. Shin zã su ce: « Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ » ?
31. Ka ce: « Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku. »
( 1 ) Wannan ãyã tanã nũna yadda wani ke cẽton wani sabõda kusanci dõmin a ƙãra Raukaka mai cẽton. Sharaɗin cẽton shĩ ne wanda ake cẽton yanã da nãsa ĩmanin. Wanda jinginarsa ta halaka bãbu mai cẽtonsa. Zuriya ta haɗa uwãye da almajiran mãlami sãlihi. Suna shiga a cikin cẽtonsa.