Hausa translation of the meaning Page No 523

Quran in Hausa Language - Page no 523 523

Suratul Al-Dhariyat from 52 to 14


52. Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: « Mai sihiri ne kõ mahaukaci. »
53. shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
54. Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
55. Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
56. Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
57. Bã Ni nufln ( sãmun ) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su ( yi Mini hidimar ) ciyar da Ni. ( 1 )
58. Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
59. To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki ( na ɗĩban zunubi ) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
60. Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
Sũratu Ɗũr
Tanã karantar da yadda ake rumãtar da abõkin husũma da hujjõji da kuma jan hankalinsa zuwa ga gaskiya.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da Ɗũr ( Dũtsen Mũsã ) .
2. Da wani littãfi rubũtacce.
3. A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.
4. Da Gidan da aka rãyar da shi ( da ibãda ) .
5. Da rufin nan da aka ɗaukaka.
6. Da tẽkun nan da aka cika ( da ruwa ) .
7. Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.
8. Bã ta da mai tunkuɗẽwa.
9. Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.
10. Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.
11. To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
12. Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.
13. Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.
14. ( A ce musu ) : « Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita. »
( 1 ) Bã Ni nufin su sãmo Mini abinci, kuma bã Ni nufin su dafa Mini abinci.