Hausa translation of the meaning Page No 525

Quran in Hausa Language - Page no 525 525

Suratul Al-Tur from 32 to 49


32. Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?
33. Shin, cẽwa suke yi: « Shi ne ke ƙãga faɗarsa » ? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.
34. Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne.
35. Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?
36. Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.
37. Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?
38. Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke ( hawa sunã ) saurãron ( lãbãrin samã ) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.
39. Shin, Yanã ( 1 ) da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?
40. Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?
41. Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?
42. Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.
43. Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!
44. Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.
45. To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.
46. Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.
47. Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba ( a nan dũniya ) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.
48. Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake ( 2 ) Ubangijinka da ( tasbĩhi ) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye ( dõmin salla kõ wani abu ) .
49. Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi ( da tasbĩhin ) dalõkacin jũyãwar taurãri.
( 1 ) Waɗansu Lãrãbawa sunãkiran Malã'iku 'ya'yan Allah mãtã, sunã kuma bauta musu dõmin su cẽce su daga Allah, suna yin gumãka da sũnansu.
( 2 ) ( Ma'anar ita ce tsarkakẽwa kõ tasbĩhi, 'tsare sallõli, farillai, anã cẽwa' faɗin « Subhãnal lãhi wal Hamdu Lillãhi » a bãyan kõwane mazauni, dõmin ya zama kaffãrar wannan mazaunin.