Hausa translation of the meaning Page No 537

Quran in Hausa Language - Page no 537 537

Suratul Al-Waqi'ah from 77 to 3


77. Lalle shi ( wannan littãfi ) , haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
78. A cikin wani littafi tsararre.
79. Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
80. Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
81. Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
82. Kuma kunã sanya arzikinku ( game da shi ) lalle kũ, ku ƙaryata ( shi ) ?
83. To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? ( Kusa da mutuwa ) .
84. Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
85. Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
86. To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
87. Ku mayar da shi ( cikin jikinsa ) har idan kun kasance mãsu gaskiya ( 1 ) .
88. To, amma idan ( mai mutuwar ) ya kasance daga makusanta,
89. Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
90. Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
91. Sai ( a ce masa ) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
92. Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
93. Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
94. Da ƙõnuwa da Jahĩm,
95. Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
96. Sabõda haka, ka tsarkake ( 2 ) sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
Sũratul Ḥadĩd
Tanã karantar da muhimmancin Jihãdi da ciyar da dũkiyadõmin Jihãdin ɗaukaka kalmar Allah, a bãyan ĩmãni da Allah da ManzonSa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
2. Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme.
3. Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme.
( 1 ) Idan kun kasance mãsu gaskiya ga da'awar rashin Tãshin Ƙiyãma, to, ku yi ƙõƙarin hana mutuwa ga mutãne dõmin ku hana cikar alkawarin tayarwa a bãyan mutuwa.
( 2 ) A cikin rukũ'i anã tasbĩhi da cẽwa: « Subhãna Rabbiyal Azĩm wa Bihamdih. » Ma'anarsa Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma game da gõde Masa.