Hausa translation of the meaning Page No 536

Quran in Hausa Language - Page no 536 536

Suratul Al-Waqi'ah from 51 to 76


51. « Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa! »
52. « Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum ( ɗanyen wutã ) . »
53. « Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta. »
54. « Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi. »
55. « Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa. »
56. Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
57. Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
58. Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
59. Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
60. Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ( 1 ) ba,
61. A kan Mu musanya waɗansu ( mutãne ) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
62. Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
63. Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
64. Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
65. Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa,sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
66. ( Kunã cẽwa ) « Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra! »
67. « Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa! »
68. Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
69. Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
70. Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
71. Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
72. Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
73. Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
74. Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
75. To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
76. Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
( 1 ) Ãyã ta 60 haɗe take da ãya ta 61 watau, bã zã Mu kãsa musanya ku da waɗansu mutãne ba su tsaya matsayinku, sa'an nan kũ kuma Mu mayar da ku wata halitta.