Hausa translation of the meaning Page No 544

Quran in Hausa Language - Page no 544 544

Suratul Al-Mujadalah from 12 to 21


12. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan zã ku gãnãwa da Manzon Allah, to, ku gabãtar da 'yar sadaka ( 1 ) a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi ( abin sadakar ba ) , to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
13. Ashe, kun ji tsõron ku gabãtar da sadakõki a gabãnin gãnãwarku? To, idan ba ku aikata ba, kuma Allah Ya kõmo da ku zuwa ga sauƙi, sai ku tsai da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa. Kuma Allah ne Mai ƙididdigewa ga abin da kuke aikatãwa.
14. Ashe, baka ga waɗanda ( 2 ) suka jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu ba, bã su cikinku, kuma bã su a cikinsu kuma sunã rantsuwa a kan ƙarya, alhãli kuwa sunã sane?
15. Allah Ya yi musu tattalin azãba mai tsanani. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana.
16. Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sabõda haka suka kange ( mũminai ) daga jihãdin ɗaukaka tafarkin Allah. To, sunã da azãba mai wulãkantãwa.
17. Dũkiyõyinsu ba su wadãtar musu kõme ba daga Allah, haka kuma ɗiyansu. Waɗannan 'yan wutã ne. Sũ, mãsu dawwama ne a cikinta.
18. Rãnar da Allah ke tãyar da su gabã ɗaya, sai su yi Masa rantsuwa kamar yadda suke yi muku rantsuwa ( a nan dũniya ) kuma sunã zaton cẽwa sũ a kan wani abu suke! To, lalle sũ, sũ ne maƙaryata.
19. Shaiɗan ya rinjaya a kansu, sai ya mantar da su ambaton Allah, waɗannan ƙungiyar Shaiɗan ne. To, lalle ƙungiyar Shaiɗan, sũ ne mãsu hasãra.
20. Lalle, waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa waɗannan sunã a cikin ( mutãne ) mafi ƙasƙanci.
21. Allah Ya rubũta cẽwa, « Lalle zan rinjãya, Nĩ da ManzanniNa. » Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.
( 1 ) Hukuncin tãyar da mutãne dõmin a gãna da Manzon Allah, bã ya halatta sai a kan larũra mai tsanani sabõdahaka aka sanya gabãtar da sadaka, sa'an nan aka sõke shida umurni da tsaron salla dõmin wa'azin da ke cikinta dakuma bayar da zakka.
( 2 ) Bãyan maganar mãsu tãyar da mutãne dõmin gãnãwa a cikin majalisa, sai kuma munãfikai mãsu mu'ãmala da kãfirai, kuma su jẽ su zauna cikin majalisar Musulmi dõmin su ɗauki rahõtonsu zuwa ga maƙiyansu.