Hausa translation of the meaning Page No 545

Quran in Hausa Language - Page no 545 545

Suratul Al-Mujadalah from 22 to 3


22. Bã zã ka sãmi mutãne mãsu yin ĩmãni da Allah da RãnarLãhira sunã sõyayya da wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa ba, kõ dã sun kasance ubanninsu ne, kõ ɗiyansu kõ 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yã rubuta ĩmãni a cikin zukãtansu, kuma Yã ƙarfafa su da wani rũhi ( 1 ) daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu babban rabo.
Sũratul Ḥashr
Tanã karantar da yadda Allah ke shirya yadda zai taimaki wanda ya dõgara a gare Shi ga bin umurninSa, da sauƙi, ta hanyar da bai sani ba.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah, alhãli kuwa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
2. Shĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi, ( 2 ) daga gidãjẽnsu da kõra ( 3 ) ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri.
3. Kuma ba dõmin Allah Ya rubuta musu kõrar ba, dã Ya azabta su a cikin dũniya, kuma a Lãhira sunã da azãbar wutã.
( 1 ) Waɗanmda suka tsare dõkokin Allah, Allah zai ba su ƙarfin rai ga zartar da al'amurransu da kyau, kuma zai wadãta su adũniya da Lãhira. Asalin rũhi shine rai. Anã nufin rãyuwar ĩmãni da ƙarfin halin fuskantar gaskiya.
( 2 ) Mazõwa Littãfi a nan, sũ ne Yahũdun Madĩna, watau Banĩ Nadĩr.
( 3 ) Kõrẽwa daga ƙasã, Annabi yã kõre su zuwa Haibara a gargaɗar farko, Umar ya kõre su daga Haibara zuwa Syria a gargaɗa ta biyu.