Hausa translation of the meaning Page No 549

Quran in Hausa Language - Page no 549 549

Suratul Al-Mumtahanah from 1 to 5


Sũratul Mumtaḥana
Tanã gargaɗi ga Musulmi su tsintsintar da biyayyarsu ga Allah, su yanke wata mu’amala da kãfirai, bã da sun zãlunce su ba.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi, 845. Kuna jẽfa sõyayya ( 1 ) zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku ( daga gidãjenku ) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya.
2. Idan sun kãma ku, zã su kasance maƙiya a gare ku, kuma su shimfiɗa hannuwansu da harsunan gũrin ku kãfirta.
3. Zumuntarku bã zã ta amfãne ku ba, haka kuma ɗiyanku, a Rãnar Kiyãma. ( Allah ) zai ( 2 ) rarrabe tsakãninku, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
4. Lalle abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrãhĩm da waɗanda ke tãre da shi a lõkacin da suka ce wa mutnensu, « Lalle mũ bãbu ruwanmu daku, kuma da abin da kuke bautãwa, baicin Allah, mun fita batunku, kuma ƙiyayya da jiyẽwa jũna sun bayyana a tsakãninmu, sai kun yi ĩmãni da Allah Shi kaɗai. » Fãce maganar Ibrãhĩm ga ubansa ( da yace ) , « Lalle za ni nẽma maka gãfara kuma ban mallaki kõme ba daga Allah sabõda kai. » « Yã Ubangijinmu! A gare Ka muka dõgara, kuma gare Ka muka mayar da al' amuranmu, kuma zuwa gare Ka makõma take. »
5. « Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu fitina ga waɗanda suka kãfirta, kuma Ka yi gãfara gare Mu. Ya Ubangijinmu! Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima! »
( 1 ) Wani Sahãbin Annabi da ake cẽwa Hãtibu bn Abi Balta'a, ya rubũta takarda zuwa ga Ƙuraishãwa yanã sanar da su cẽwa Annabi na zuwa garinsu da yãƙi, sai Allah Ya sanar da Annabi tun manzonsa bai isa ba ga Ƙuraishãwa, sai aka mayar da takardar. Da aka tambayi Hãtibu dalĩlin yin ta,sai ya ce dõmin yanã da ɗiya da dũkiya ne a can, dõmin haka ya so ya gaya musu zuwan Annabi kõ da yake yanã da cikakken ĩmãmin cẽwa Annabi gaskiya ne, kuma zai rinjãye su duk yadda aka yi. Sai Annabi ya karɓi uzurinsa, ba a yi masa kõme ba, sai dai abin da Allah Ya hana; kada Musulmi su sãke wata ma'amala da kãfirai a ɓõye, koa bayyane sabõda dalĩlan da aka faɗa a cikin sũrar.
( 2 ) Ga wata ƙirã'ã zã a fassara wurin da cẽwa, za a rarrabe tsakãninku;