Hausa translation of the meaning Page No 550

Quran in Hausa Language - Page no 550 550

Suratul Al-Mumtahanah from 6 to 11


6. Lalle, haƙĩƙa, abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku daga cikinsu, ga wanda ya kasance yanã fãtan ( rahamar ) Allah da Rãnar Lãhira, kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne wadãtacce, Gõdadde.
7. Anã tsammãnin Allah Ya sanya, a tsakãninku da tsakãnin waɗanda kuka yi ƙiyayya da su, wata sõyaya daga gare su, kuma Allah Mai ĩkon yi ne, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
8. Allah bã Ya hana ku, daga waɗanda ba su yãƙe ku ba sabõda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidãjenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu ãdalci. Lalle Allah Yanã son mãsu ãdalci.
9. Allah Yanã hana ku kawai daga waɗanda suka yãke ku sabõda addini kuma suka fitar da ku daga gidãjenku, kuma suka taimaki jũna ga fitar da ku, karku jiɓince su, kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan sũ ne azzãlumai.
10. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan mãtã mũminai suka zo muku, sunã mãsu hijira, to, ku jarraba su. Allah Shĩ ne mafi sani ga ĩmãninsu. To, idan kun san sũ mũminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kãfirai. Sũ mãtan bã su halatta ga aurensu, sũ kuma kãfiran bã su halatta ga auren mãtan. Ku bã su abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma bãbu laifi a kanku ga ku aure su idan kun bã su sadãkõkinsu. Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai, kuma ku tambayi abin da kuka ɓatar daga dũkiya, su kuma kãfirai su tambayi abin da suka ɓatar na dũkiya. Wannan hukuncin Allah ne Yanã hukunci a tsakãninku. kuma Allah, Masani ne, Mai hikima
11. Kuma idan wani abu ya kuɓuce muku daga mãtanku zuwa ga kãfirai sa'an nan kuma kuka ɗauki fansa, to, sai ku bai wa waɗanda matansu suka tafi kwatankwacin abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma ku yi biyayya da taƙawa ga Allah wanda kuke mãsu ĩmãni da Shi, Shi Kaɗai.