Hausa translation of the meaning Page No 548

Quran in Hausa Language - Page no 548 548

Suratul Al-Hashr from 17 to 24


17. Sai ãƙibarsu ta kasance cẽwa su biyun duka sunã a cikin wutã, mãsu dawwama cikinta. « Kuma wannan shĩ ne sakamakon mãsu zãlunci. »
18. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa. ( 1 )
19. Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rãyu, kansu. Waɗannan sũ ne fãsiƙai.
20. 'Yan Wutã da 'yan Aljanna bã su daidaita. 'Yan Aljanna, sũ ne mãsu babban rabo.
21. Dã Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dũtse, dã lalle kã ga dũtsen yanã mai tawãli'u, mai tsattsãgẽwa sabõda tsõron Allah, kuma waɗancan misãlai Munã bayyana su ne ga mutãne, da fatan za su yi tunãni.
22. ( Wanda Ya saukar da Alƙur'ani ) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai.
23. Shĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai tĩ1astãwa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi.
24. Shĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa.Yanã da sũnãye mãsu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi,Mai hikima.
( 1 ) Daga wannan ãyã ta l8 zuwaƙarshen sũra, yanã bayãnin hãsilin darasin sũrar ne dunƙule, da kuma ambatar muhimman abũbuwan da ta ƙunsa dõmin wa'azi da farkarwa ga mai hankali.