Hausa translation of the meaning Page No 555

Quran in Hausa Language - Page no 555 555

Suratul Al-Munafiqun from 5 to 11


5. Kuma idan aka ce musu « Ku zo Manzon Allah ya nẽma maku gãfara, » Sai su gyãɗa kãwunansu, kuma ka gan su sunã kangẽwa, alhãli kuwa sunã mãsu girman kai.
6. Daidai ne a kansu, kã nẽma musu gãfara kõ ba ka nẽmamusu ba. faufau Allah bã zai gãfarta musu ba. Lalle Allah, bã zai shiryar da mutãne fãsiƙai ba.
7. Sũ ne waɗanda ke cẽwa « Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su wãtse, » alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã su fahimta.
8. Sunã cẽwa « Lalle ne idan mun kõma ( 1 ) zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba. »
9. Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da ɗiyanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
10. Kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gãbanin mutuwa ta je wa ɗayanku har ya ce: « Yã Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci dõmin in gaskata kuma in kasance daga sãlihai? »
11. Kuma Allah bã zai jinkirta wa wani rai ba idan ajalinsa ya je. Kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa.
( 1 ) Abdullah bn Ubayyi bn Salũl ya faɗi cẽwa « Wallahi idan mun kõma Madĩna wanda ya fi ƙarfi, lalle zai fitar da wanda ya fi ƙasƙanci. » Yanã nufin Ansãrai mutãnen Madĩna zã su kõri Muhãjirai. Yã faɗi haka a cikin wata tafiya ta jihãdi. Aka gaya wa Annabi, sai ya yi musu. Allah Ya kunyata shi.