Hausa translation of the meaning Page No 554

Quran in Hausa Language - Page no 554 554

Suratul Al-Jumu'ah from 9 to 4


9. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni ! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ( 1 ) ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
10. Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban rabo.
11. Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: « Abin da yake a wurin Allah ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrinmãsu arzũtãwa. »
Sũratul Munãfiƙũn
Tanã karantar da halãyen munãfukan Madĩna a zãmanin Annabi da wa’azi ga barin yin hãli irin nãsu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Idan munãfukai ( 2 ) suka jẽ maka suka ce: « Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah ne, » Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa ManzonSa ne, kuma Allah Yanã shaida lalle munafukan haƙĩƙa , maƙaryata ne.
2. Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sai suka taushe daga tafarkin Allah. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana.
3. Wancan, dõmin lalle sũ, sun yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sai aka yunƙe a kan zukãtansu. Sabõda sũ, bã su fahimta.
4. Kuma idan kã gan su, sai jikunansu su bã ka sha'awa kuma idan sun faɗa, ( 3 ) zã ka saurãra ga maganarsu. Kamar dai sũ ƙyami ne wanda aka jingine. Sunã zaton kõwace tsãwa a kansu take. Sũ ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Yã la'ane su. Yãya ake karkatar da su?
( 1 ) Ba a hana Musulmi aiki ba a kõwace rãna, sai dai an hana duk wanda Jumu'a ta lazimta a kansa da ya yi wani aiki wanda bã na tattalin salla ba a rãnar Jumma'a, a bãyan kiran salla. Anã nufi da kiran salla na biyu a bãyan limãmi ya zauna a kan mumbarinsa, dõmin wannan kiran aka sani azãmanin Annabi da Abubakar da Umar. Amma kira na farko, Usman bn Affãn ne ya fãra shi dõmin farkar da mutãne, a bãyan sun yi yawa kuma sun kama sana'õ'i. Kuma a bãyan an ƙãre salla, sai a wãtse zuwa ga ayyuka da nẽman abinci. Bã a tsayãwa yin wata nãfila a bãyan sallarJumu'a, sai dai an so yin raka'a biyu a bãyan fita daga masallãci kamar yadda Annabi ke yi. A farko, anã yin huɗubar sallar Jumma'a a bãyan salla har a lõkacin da ãyarin Dihya el Kalbi ya kõmo daga shãm ( Syria ) da abinci,ya sauka a Baƙĩ'a, suka buga ganga, sai Sahabbai suka fita dõmin nẽman sayen abincin a gabãnin a ƙãre huɗubar suka bar mutum gõma shã biyu tãre da Annabi. Sai akamayar da huɗubar a gabãnin salla. Kuma an fahimcicẽwa anã yin huɗuba atsaye. Kuma ba a kafa Jumu'a, sai a kafaffen gari, amma Jumu'a nã ƙulluwa da mutum gõma sha biyu da lĩman.
( 2 ) Munãfuki, a zãmanin Annabi, shahãda, ya bayyana Musulunci, amma kuma a ɓõye Shĩ kãfiri ne. A bãyan Annabi anã cẽwa munãfuki zindĩƙi.
( 3 ) Munãfukai sunã da kyaun sũrar jiki kuma sun iya magana da fasaha amma fa bã su da hankali sabõda ƙaryar da suke a kanta, sabõda hakasunã tsõron kõwane irin mõtsi ya zama a kansu.