Hausa translation of the meaning Page No 556

Quran in Hausa Language - Page no 556 556

Suratul Al-Taghabun from 1 to 9


Sũratut Tagãbun
Tanã karantar da cẽwa wanda ya shagala da dũniya ya bar addini, ya yi hasara. Addini kuwa shi ne bin umurnin Allah da barin haninSa ga kõme.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon yi ne.
2. Shĩ ne wanda Ya halitta ku. Sa'an nan daga gare ku akwai kãfiri kuma daga gare ku akwai mũmini. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
3. Ya halitta sammai da ƙasã da abin da yake hakkinSa. Kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku. Kuma zuwa gare Shi makõma take.
4. Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasã. Kuma Yanã sanin abin da kuke bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.
5. Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi?
6. Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: « Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ? » Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu ( daga gare su ) . Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde.
7. Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: « Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne. »
8. Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne.
9. A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma.