Hausa translation of the meaning Page No 558

Quran in Hausa Language - Page no 558 558

Suratul Al-Talaq from 1 to 5


Sũratut Ɗalãƙ
Tanã karantar da hukunce- hukuncen sakin mãtan aure da haƙƙõkin da ke rãtayuwa ga ma’auran a bãyan sakin.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu, ( 1 ) kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bãyan haka.
2. Sa'an nan idan sun isa ga ajalinsu ( na idda ) sai ku riƙe su da abin da aka sani kõ ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da mãsu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar dõmin Allah. Wancan ɗinku anã yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yanã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita.
3. Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme.
4. Kuma waɗanda suka yanke ( 2 ) ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, ( shi ne ) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, ( Allah ) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa.
5. Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sãkamako.
( 1 ) Saki, shĩ ne warware ƙullin halaccin sãduwa da jũna a tsakãnin miji da mãta. Haƙƙi ne wanda Allah Ya saka ga hannayen maza ban da mãtã. saki ga idda, watau yasake ta saki gudã a cikin tsarkin dabai shãfe ta ba dõmin sauƙin idda. Yanã haramta ga mijin da mãtar ya fitar da ita kõ ta fita daga ɗãkinta a lõkacin idda. fãruwar wani al'amari shi ne sõyayya a bãyan ƙiyayya da mayarwa a bãyan saki. Alfãsha a nan, tanã nufin faɗa da zãge- zãge a kan surukantã. Anã fitar da mai iddar saki sabõda alfãsha daga gidanta.Akwai saki na sunna kuma akwai na bidi'a, amma saki na sunna ɗaya ne, a cikin tsarkin da bã a shãfe ta ba kuma kada a ƙãra mata wani saki har ta ƙãre idda, sakin bidi'a kuwa shĩne uku gabã ɗaya kõ a cikin idda gudã, a cikin haila kõ jinin bĩƙi. Sakin bidi'a yanã 1azimta, Anã tĩlastã shi mayarwa ga wadda aka saki a cikin haila idan bai kaiuku ba ga miji 'yantacce, kõ biyu ga miji bãwã.
( 2 ) Muddar idda ga wadda ta yanke ɗammãnin haila, sabõda tsũfa, watanni uku,kuma bã zã ta ƙãra kõme ba a kai. Wadda take akwai shakka a game da ita ga kõ akwai cikikõ bãbu shi, to, zã ta yi iddar wattani uku kuma ta yi jiran watanni tara, watau ta yi watannin shẽkara, uku na idda, sauarã na ta fidda shakkãne. Haka ne hukuncin mai istihãla, watau jinin ciwo. Amma yãrinya mai shakkar ciki, sai ta zauna har shakka ta gushe. Yarinyar da ba ta fãra haila ba tana iddar wata uku. Bãbu bambanci a tsakãnin ɗiya da baiwa ga idda da watanni, amma ga idda ta tsarki, to, baiwã tana yin rabin naɗiya ga saki da mutuwa.