Hausa translation of the meaning Page No 557

Quran in Hausa Language - Page no 557 557

Suratul Al-Taghabun from 10 to 18


10. Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyinMu, waɗannan sũne'yan wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita.
11. Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah,Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne.
12. Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan ManzonMu.
13. Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara.
14. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi ( 1 ) a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
15. Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina ( 2 ) ɗai ne. Kuma Allah, a wurinSa akwai wani sakamako mai girma.
16. Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
17. Idan kun bai wa Allah rance, rance mai kyau, ( Allah ) zai ninka shi a gare ku kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai yawan gõdiya ne, Mai haƙuri.
18. Shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai hikima.
( 1 ) Maƙiyi, shĩ ne mai hana mutumin da yake ƙiyayya da shi wani alhẽri ya sadu da shi. Idan son dũkiya kõ mãtakõ ɗiya ya hana mutum yin sadaka kõ fita zuwa jihãdji, to, dũkiyar da mãtan da ɗiyan sun zama maƙiyansa ke nan.
( 2 ) Fitina, ita ce duk abin da zai cũci mutum ta hanyar da yake amincẽwa, cũtar ta dũniya ce kõ ta Lãhira. Cũtar Lãhira ta fi tsanani sabõda girman hasãrar da ke a cikinta.