Hausa translation of the meaning Page No 559

Quran in Hausa Language - Page no 559 559

Suratul Al-Talaq from 6 to 12


6. Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar ( 1 ) daga gwargwadon sãmunku. Kuma kada ku cũce su dõmin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abũta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shãyar da mãma sabõda ku, sai ku bã su tsãdõdinsu. Kuma ku yi shãwara a tsakãninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nũna talauci to wata mace zã ta shãyar da mãma sabõda shi ( mijin ) .
7. Sai mawadãci ya ciyar daga wadãtarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bã shi. Allah bã Ya kallafa wa wani rai fãce abin da Ya bã shi. Allah zai sanya sauƙi a bãyan tsanani.
8. Kuma da yawa ( 2 ) daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisãbi, hisãbi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azãba abar ƙyãma.
9. Sa'an nan ta ɗanɗana masĩfar al'amarinta. kuma ƙarshen al'amarinta ya kasance hasãra,
10. Allah Ya yi musu tattalin wata azãba mai tsanani. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abũta hankula, waɗanda suka yi ĩmãni! Haƙĩƙa Allah Ya saukar da wata tunãtarwa zuwa gare ku.
11. Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashnsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata ( 3 ) masa arziki.
12. Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasã kwatankwacinsu, umuruinSa yanã ta sauka a tsakaninsu dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõme, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõme da sani.
( 1 ) Mijin zai fita ya bar wa mãtar da ya saki ɗaki ta zauna a ɗakinta har ta ƙãre idda. Anã ciyar da mai sakin kõmẽ, amma bã a ciyar da mai sakin bã'ini sai idan tanã da ciki. Ijãrar shãyarwa tanã akan uba ga uwar da aka saki saki bã'ini kõ ga watarta, bisa ga yardar sassan biyu.
( 2 ) A bãyan da ya gama bayãninsaki da hukunce- hukuncen da suka rãtayu a gare shi, sai kuma ya gõya gargaɗi ga wanda bai bi waɗannan hukunce- hukuncen ba, ta hanyar tsoratar da shi da cẽwa Allah Ya halaka alƙaryu mãsu yawa sabõda sãɓã Masa ga hukunce- hukuncenSa ga ƙanãnan abũbuwa, balle mutum guda wanda ya sãɓã masa ga babban al'amari kamar aure da saki waɗanda rãyuwar ɗan Adam ta dõgara a kansu kuma ya yi bushãra ga wanda ya bĩ shi da taƙawa, ya fita daga duhun al'ãdu zuga ga hasken sharĩ'arSa, kuma Ya yi wa'adi da bã shi sauƙin rãyuwa daga wadãtarSa mai yawa.
( 3 ) Allah Yã kyautata wa wanda ya tsare sharĩ'arsa da kyau, awajen arzikinsa tun daga dũniya har ya zuwa Lãhira, dõmin Yã ce: « Haƙĩƙa Allah Yã kyautatã masa ( mai tsare sharĩ'ar ) arziki, » bã da Yã yi ƙaidin lõkaci kõ wuri ba.