Hausa translation of the meaning Page No 56

Quran in Hausa Language - Page no 56 56

Suratul Al-Imran from 46 to 52


46. « Kuma yana yi wa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma lõkacin da yana dattijo, kuma yana daga sãlihai. »
47. Ta ce: « Yã Ubangijina! Yãya yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba? » ( Allah ) Ya ce: « Kamar wannan ne, Allah yana halittar abin da Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, » Ka kasance!, Sai yana kasancẽwa. « »
48. Kuma Ya sanar da shi rubũtu da hikima da Taurata da injĩla.
49. Kuma ( Ya sanya shi ) manzo zuwa ga Bani Isrãila'ĩla ( da sãko, cẽwa ) , Lalle ne, ni haƙĩƙa nã zõ muku, da wata ãyã daga Ubangijinku. Lalle ne ni ina halitta muku daga lãka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hũra a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makãho da kuturu, kuma ina rãyar da matottu, da izibin Allah. Kuma ina gayã muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyẽwa acikin gidãjenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyã a gare ku, idan kun kasance mãsu yin ĩmãni.
50. « Kuma inã mai gaskatãwa ga abin da yake a gabãnina daga Taurata. Kuma ( nãzo ) dõmin in halatta muku sãshen abin da aka haramta muku. Kuma nã tafo muku da wata ãyã daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. »
51. « Lalle Allah shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan ce hanya madaidaiciya. »
52. To, a lõkacin da Ĩsa ya gane kãfirci daga gare su, sai ya ce: « Su wãne ne mataimakãna zuwa ga Allah? » Hawãriyãwa suka ce: « Mu ne mataimakan Allah. Mun yi ĩmani da Allah. Kuma ka shaida cẽwa lalle ne mu, mãsu sallamãwa ne.»