Hausa translation of the meaning Page No 55

Quran in Hausa Language - Page no 55 55

Suratul Al-Imran from 38 to 45


38. A can ne Zakariyya ya rõki Ubangijinsa, ya ce: « Ya Ubangijina! Ka bã ni zuriyya mai kyau daga gunKa. Lalle ne Kai Mai jin addu'a Kake. »
39. Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin masallãci. ( Suka ce ) , « Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga sãlihai. »
40. Ya ce: « Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya sãme ni,kuma mãtãta bakarãriya ce? » Allah ya ce, « Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so. »
41. Ya ce: « Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma! » ( Allah ) Ya ce « Alãmarka ita ce ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe. »
42. Kuma a lõkacin da malã'iku suka ce: « Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zãɓe ki, kuma Ya tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan mãtan tãlikai. »
43. « Yã Maryamu! Ki yi ƙanƙan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi rukũ'i tãre ( 1 ) da mãsu rukũ'i. »
44. Wannan yana daga lãbarun ( 2 ) gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka ( Muhammadu ) . Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu ( domin ƙuri'a ) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma ( 3 ) .
45. A lõkacin da malã'iku suka ce « Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta. »
( 1 ) Wannan ya nũna muhimmancin salla tãre da jama'a masallaci, kõ da ga mãta. Sai dai hãli ya nũna an fi son mace ta yi salla a ɗakinta.
( 2 ) Wannan yana daga cikin dalĩlan annabcin Annabi Muhammad, tsira da aminci su tabbata a gare shi, wajen faɗar lãbãrin abin da bai halarta ba.
( 3 ) Uwar Maryamu tã ɗauke ta, tã kai ta ga Bani kãhin ɗan Hãrũna ɗan'uwan MũSã, a lõkacin nan, sũ ne suke tsaron Baitil Muƙaddas, ta mĩka musu ita, ta ce: « Ku karɓa. Na 'yantar da ita, kuma mace mai haila bã ta shiga masallaci, kuma bã zan mayar da ita a gidanã ba. » Sai suka ce: « Wannan ɗiyar limãminmu ce kuma shugaban Ƙurbãninmu. » Zakariyya ya ce: « Ku bã ni ita dõmin innarta tanã tãre da ni. » Su ka ce: « Rãyukanmu bã su iya barin ta ga wani. » Sai suka yi ƙuri'a da alƙalumansu da suke rubũtun Attaura da su. Sai Zakariyya ya rinjãya. An ce sun tafi kõgin Urdun ne suka jẽfa alƙaluman nãsu, a kan cẽwa wanda alƙalaminsa bai bi ruwa ba, ya tsaya, shĩ ne ya rinjãya. Sai Zakariyya ya rinjãya, ga shi kuma shĩ ne shugabansu, kuma mallminsu, kuma annabinsu, sai ya sanya ta a cikin bẽne, a cikin masallacinsa.