Hausa translation of the meaning Page No 57

Quran in Hausa Language - Page no 57 57

Suratul Al-Imran from 53 to 61


53. « Yã Ubangijinmu! Mun yi imãni da abin da Ka saukar, kuma mun bi ManzonKa, sai Ka rubũta mu tãre da mãsu shaida. ( 1 ) . »
54. Kuma ( Kãfirai ) suka yi mãkirci, Allah kuma Ya yi musu ( sakamakon ) makircin, kuma Allah ne Mafi alhẽrin mãsu sãka wamãkirci.
55. A lõkacin da Ubangiji Ya ce: « Ya Ĩsa! Lalle NĨ Mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kãfirta, kuma Mai sanya waɗanda suka bĩ ka a bisa waɗanda suka kãfirta har Rãnar Ƙiyãma. Sa'an nan kuma zuwa gare Ni makõmarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakãninku, a cikin abin da kuka kasance kuna sãɓã wa jũna. »
56. « To, amma waɗanda suka kãfirta sai In azabta su da azãba mai tsanani, a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mãsu taimako. »
57. Kuma amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sai ( Allah ) Ya cikã musu ijãrõrinsu. Kuma Allah bã Ya son azzãlumai.
58. « Wannan Muna karanta shi a gare ka ( Muhammad ) daga ãyõyi, da Tunatarwa mai hikima ( Alƙur'ãni ) . »
59. Lalle ne misãlin Ĩsã a wurin Allah kamar misãlin Ãdama ne, ( Allah ) Yã halitta shi daga turɓãya, sa'an nan kuma Ya ce masa: « Ka kasance: » Sai yana kasancewa.
60. Gaskiya daga Ubangijinka take sabõda haka kada ka kasance daga mãsu shakka.
61. To, wanda ya yi musu ( 2 ) da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: « Ku zo mu kirãyi, 'yã'yanmu da 'yã'yanku da mãtanmu da mãtanku da kanmu da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar, Allah a kan maƙaryata. »
( 1 ) Masu shaida su ne Musulmidõmin a cikin Attaura sũnansu mãsu shaida, mabiya Annabi Ummiyyi.
( 2 ) Wanda ya yi hujjacẽwa da Annabi a kan sha'anin Ĩsã; kamar Nasãran Najrãn, sun tafi dõmin su yi jãyayya da Annabi. Ya kira su zuwa ga mubãhala, suka ce: sai sun yi shãwara, suka ce wa jũnansu: « Kun san gaskiya mutumin nan Annabi ne. Ku bar ra'ayinku na mubãhala, dõmin wani Annabi bai taɓa yin ta tãre da wasu mutãne ba, fãce sun halaka. » Bãyan haka suka iske Annabi yã fito shi da Hasan da Husaini da Fãtima da Ali, kuma ya ce musu: « ldan na yi addu'a ku ce, Ãmin. » Sai suka ƙi mubahãlar, suka yi sulhu akan jizya.